BASHI DA RABO WANDA BAI YI AIKI N DA ZA A GAFARTA MASA BA CIKIN WATAN RAMADAN WATA MAI ALBARKA

BASHI DA RABO WANDA BAI YI AIKI N DA ZA A GAFARTA MASA BA CIKIN WATAN RAMADAN WATA MAI ALBARKA


Wata rana Manzon Allah S.A.W Zai hau kan banbarinsa yayi huduba ya dora kafarsa kenan akan matattakala ta farko sai Mala'ika Jibril yazo masa ya ce masa duk mutumin daya rayu da iyayansa bai samu Aljannah ta karkashin su ba Allah ya tsine masa, sai Annabi S.A.W Yace Ameen
Sai ya kara cewa duk mutumin da watan ramadan yazo bai yi wani aiki da Allah zai gafarta masa ba shima Allah ya tsine masa, sai Annabi S.A.W yace Ameen
Sai Mala'ika jibril (A.S) ya kara cewa kuma duk mutumin da aka ambaci sunnanka bayyi maka salati ba shima Allah ya tsine masa, sai Manzon Allah S.A.W yace Ameen
Al-muhin dai watan ramadan yana da falaloli wadanda baza su kirgu ba dan haka sai mu dage munemi yardar Allah acikinsa kuma munisanci duk wani abu da zai sa muyi shi har azumun mu ya dan jikkata muyi kisshiR ruwan banza dawofi.
Falalar Azumin Watan Ramadan
1. Ana bude kofofin sama wato aljannah a kuma rufe na wuta a kuma daure kan gararrun aljanu
2. kuma dukkan dare Allah S..W.T yana yanta bayinsa daga wuta a kowanna daren azumi harkarshen watan azumi
3. Ana nunnunka aiyuka masu kyau zuwa nunkin baninki har watan ya mutu
4. kuma watan azumi ne da ake dacewa da daran lailatul qadri wanda darajar sa agun Allah .S.W.T yafi dare dubu
5. Sannan ladan azumi Allah .S.W.T shi kadaine zaiba da ladan a zumi sabanin ragowar ibada
6. A watan azumine in akai tsayuwar dare Allah swt yake gafartawa mutum zunubin dayai abaya
Yan uwa akwai falalar azumi dayawa amma musani cewa fa bazamu samu wadannan falalolin ba har sai mun nisanci dukkan wasu abubuwa da mukasan ba dai-dai bane, kuma munsan cewa addu'ar mala'ika kar6a66iya ce agurin Allah dan haka sai muyi ayyukan da za a gafarta mana.
Allah kasa musiffantu da ayyuka na kwarai cikin wannan wata mai albarka katsaremu daga cikin wannan tsinuwa ta mala'ika, kasamu cikin 'yan tattun bayinka
Next
This is the most recent post.
Older Post

No comments:

Post a Comment